Real Madrid ta hau kan teburin La Liga bayan cin Cadiz

Minti 30 ana tsaka da wasa Karim Benzema ya fara ci wa Real Madrid kwallo

 

Real Madrid ta je ta doke Cadiz da ci 3-0 a wasan mako na 31 a gasar La Liga da suka fafata ranar Laraba.

Minti 30 ana tsaka da wasa Karim Benzema ya fara ci wa Real Madrid kwallo a bugun daga kai sai mai tsaraon raga.

Minti uku tsakani Alvaro odriozola ya ci na biyu, saura minti biyar su tafi hutu Karim Benzema ya kara na uku, kuma na biyu da ya ci a wasan.

Da wannan Sakamakon Real Madrid ta koma ta daya a kan teburi da maki 70 iri daya da wanda Atletico keda shi.

Real ta samu wannan damar, bayan da ta yi nasara a kan Atletico a haduwar da suka yi, inda ta ci 2-1 a gida, sannan ta tashi 1-1 a Atletico.

Idan ba haka ba Atletico ta zura kwallo 57 aka zura mata 20, ita kuwa Real 56 ta zura a raga aka ci ta 24.

Sai dai ranar Alhamis Atletico Madrid za ta yi wasan mako na 31, inda za ta karbi bakuncin Huesca, wadda suka tashi 0-0 a wasan farko.

A dai ranar Alhamis Getafe za ta ziyarci Barcelona wadda ta lashe Copa del Rey na bana.

Barcelona wadda ta buga wasa 30 tana ta hudu a kan teburi da maki 65, Sevilla ce ta uku mai maki 67, bayan da ta yi karawa 32 a gasar bana.

Source: bbc.com

About admin

Check Also

Spotify Unites Football and Music In Coldplay Shirt Swap for El Clásico

  Spotify is once again bringing together record-breaking legends from the worlds of music and …

2024/25 Ghana Premier League: Week 2 Match Report – Asante Kotoko 1-0 Nsoatreman

Asante Kotoko secured their second win of the season with a 1-0 victory over 10-man …